ABUN NEMA YASAMU GA MUSULMIN DUNIYA.
Ministan Harkokin Wajen Iran Jawad Zarif ya bayyana cewa, a shirye suke da su kusanci Saudiyya. A tattaunawar da Zarif ya yi da 'yan jaridu a Dimashk Babban Birnin Siriya ya bayyana cewa, "A koyaushe a shirye muke da mu kulla kyakkyawar alaka da Saudiyya". A watan da ya gabata gwamnatin Iraki ta bayyana shiga tsakanin Saudiyya da Iran inda ake kuma ci gaba da tattaunawa a tsakanin bangarorin 2. A baya Yariman Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya tattauna da wata tashar talabijin inda ya bayyana cewa, suna da sha'awar kulla kyakkyawar dangantaka da Iran. Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewar, sun gamsu da jin dadin kalaman na Yarima bin Salman. Alakar kasashen 2 ta sakwarkwace a shekarar 2016 bayan da Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa kan wani Malamin Shi'a Nimr Al-Nimri, kuma sakamakon martanin da Iran ta mayar da kaiwa jami'an diplomasiyyar Saudiyya hari a Tehran ya sanya lamarin ya kara munana tare da yanke huldar jakadanci a tsakaninsu.