ANYI ZANGA ZANGAR KIN JININ ISRA,ILA A TURKIYYA
A fadin kasar Turkiyya an gudanar da zanga-zangar la'antar Isra'ila kan yadda take kai hare-haren ta'addanci kan Falasdinawa a Gabashin Kudus da kuma yunkurin korar Falasdinawa ta karfi da yaji daga unguwar Shaikh Jarrah a yankin.
Kungiyar Matasan Anatoliya ta jagoranci taruwar jama'a a gaban karamin ofishin jakadancin Isra'ila dake Istanbul inda aka karanta Alkur'ani Mai Tsarki a wajen.
Masu zanga-zangar dauke da tutar Falasdin sun dinga cewa, "Mun sadaukar da rayukanmu da jininmu ga Aksa" da kuma "Allah Ya tsinewa Isra'ila".
Shugaban Kungiyar a Istanbul Yunus Genc ya shaida cewa, Masallacin Aksa na da babban matsayi ga Musulmai.
A garin Elazig ma kungiyar kwadago ta ma'aikatan gwamnati ta shirya zanga-zangar la'antar Isra'ila. An daga tutar Falasdin a jerin gwanon motocin da aka yi.
Dubunnan jama'ar Malatya ma sun taru tare yin tofin Alla tsine ga Isra'ila sakamakon hare-haren da take kaiwa Falasdinawa, sun kuma nuna goyon baya ga Falasdinawa.
A garuruwan Turkiyya da dama an gudanar da zanga-zangar la'antar Isra'ila sakamakon kaiwa Falasdinawa hare-haren ta'addanci.
Comments
Post a Comment