Posts

PDP TANA ZARGIN GWAMNATIN BUHARI DA SATAR NAIRA TILIRIYAN 14

Image
Jam,iyyar PDP mai adawa da gwamnatin Nigeria tace tana zargin gwamnatin buhari da satar Naira tiriliyan 14 a shekara 4 Kacal

TALIBAN TACE TA YAFEWA KOWA

Image
Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba. A taron manema da take gudanar yanzu haka, mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana a gaban 'yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko, ya ce sun 'yantar da kasar "bayana shekaru 20 na fafutika kuma mun kori 'yan kasashen waje". "Wannan lokaci ne na alfahari," in ji shi. "Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe, " a cewarsa Mujahid

ALI KUMAINI YA AMINCE DA SABON SHUGABAN IRAN IBRAHIM REISI

Image
Ali Khamenei ya amince da kasancewar Ibrahim Reisi a matsayin sabon shugaban kasar Iran a makon da ya gabata, wanda ya baiwa Ibrahim Reisi damar fara aiki bayan bukukuwan da aka gudanar. Daga bisani kuma bikin rantsarwar da aka gudanar a majalisar Shura ya baiwa shugaban cikekken damar kama ragnar mulkin kasar. A lokacin yakin neman zabe, zabebben shugaban ya yi alkawarin bunkasa hulda da kasashen dake makwabtaka da lran tare da kuma inganta fannonin kasar da dama. Bayan lashe zabe a jawabin da ya yi da manema labarai ya yi alkawarin daidaito da Saudiyya. Haka kuma ana cigaba da wannan daidaitawa da shiga tsakanin lraki. A sabanin haka anga kuma yadda mayaka yan shi'a suna ayyuka a Siriya da lraki. Abubuwa kamar hare-hare da killacewar da kungiyoyin da Iran ke marawa baya a Daraa ke yi da kuma ayyukan dakarun kare juyin juya halin lran suka fara na tono rami a birnin Palmyra na nuna cewa tasirin Iran a Siriya zai karu a mulkin Ibrahim Reisi. Ci gaban da Rasha za ta yi na zamanantar...

DA DUMI DUMI

Image
Mayakan taliban na gabda karbe iko ga kasar 

KISAN GILLA A JOS.

Image
Anyiwa wasu matafiya musulmi kisan gilla a kan hanyar jos, bayan da suka dawowar su daga wani taron mauludi a jihar bauchi,  Tambaya??? Suwaye da alhakin wannan kisan ta,addanci?  Boko Haram ko yan kinnafin ko.. .....  

RASHA DA CHINA ZASU GUDANAR ATISAYEN SOJOJI NA HADIN GWAIWA.

Image
An ba da rahoton cewa sojojin Rasha da China za su gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa a watan gobe. A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Tsaro ta Rasha ta fitar, an bayyana cewa, wasu rundunoni daga sojojin Rasha za su halarci atisayen soja na "Interaction-2021", wanda za a gudanar a kasar Chına a tsakiyar watan Agusta. An bayyana cewa kimanin sojoji dubu 10 za su halarci atisayen hadin gwiwar, an kuma jaddawa cewa jiragen sama na sojoji da motoci masu sulke ne za'a yi amfani dasu. "Manufar atisayen ita ce karfafa huldar dake tsakanin Rasha da China, kawancen hadin gwiwa da mu'amala bisa manyan tsare-tsare, don kara matsayin hadin gwiwa a fannin soja da kawance tsakanin rundunonin sojojin kasashen biyu, don nuna jajircewa da kuma karfin Rasha da China na yaki."