ALI KUMAINI YA AMINCE DA SABON SHUGABAN IRAN IBRAHIM REISI
Ali Khamenei ya amince da kasancewar Ibrahim Reisi a matsayin sabon shugaban kasar Iran a makon da ya gabata, wanda ya baiwa Ibrahim Reisi damar fara aiki bayan bukukuwan da aka gudanar. Daga bisani kuma bikin rantsarwar da aka gudanar a majalisar Shura ya baiwa shugaban cikekken damar kama ragnar mulkin kasar. A lokacin yakin neman zabe, zabebben shugaban ya yi alkawarin bunkasa hulda da kasashen dake makwabtaka da lran tare da kuma inganta fannonin kasar da dama. Bayan lashe zabe a jawabin da ya yi da manema labarai ya yi alkawarin daidaito da Saudiyya. Haka kuma ana cigaba da wannan daidaitawa da shiga tsakanin lraki. A sabanin haka anga kuma yadda mayaka yan shi'a suna ayyuka a Siriya da lraki. Abubuwa kamar hare-hare da killacewar da kungiyoyin da Iran ke marawa baya a Daraa ke yi da kuma ayyukan dakarun kare juyin juya halin lran suka fara na tono rami a birnin Palmyra na nuna cewa tasirin Iran a Siriya zai karu a mulkin Ibrahim Reisi. Ci gaban da Rasha za ta yi na zamanantar...
Comments
Post a Comment