Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar kowanne dan kasar Afghanistan ya samu damar walwala tana mai cewa ba ta bukatar abokan gaba. A taron manema da take gudanar yanzu haka, mai magana da yawun kungiyar Zabihullah Mujahid, wanda ya bayyana a gaban 'yan jarida a karon farko tun bayan da suka kwace iko, ya ce sun 'yantar da kasar "bayana shekaru 20 na fafutika kuma mun kori 'yan kasashen waje". "Wannan lokaci ne na alfahari," in ji shi. "Muna son tabbatar da ganin Afghanistan ba ta sake tsunduma cikin yaki ba. Mun yafe wa dukkan mutanen da suka yake mu. Gaba ta zo karshe, " a cewarsa Mujahid